Latest News

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Nassarawa Ta Haramta Zanga-zanga

Rundunar Ƴan Sandan jihar Nassarawa ta haramta zanga-zanga Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta sanar da jama’a cewa an haramta duk wata zanga-zanga a fadin jihar. Rundunar ta dauki wannan matakin ne domin hana tabarbarewar doka da oda da kuma dorewar zaman lafiya da ake samu a jihar a halin yanzu tare da shawartar Iyaye dasu kula da tarbiyyar ‘ya’yansu da bawa unguwanninsu karya. Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ƴan sandan jihar Nassarawa DSP Ramhan Nansel ya bayyana cewar duk wanda aka kama da kin bin wannan umurnin doka zata yi aiki a kansa.

Yadda Ɗakuna 6 Suka ƙone ƙurmus A Wani Gida Dake Sheka Aci Lafiya A Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da tashin wata wuta a unguwar Sheka Aci Lafiya, da kuma aikin wucin gadi a matatar Mai dake Hotoro NNPC Deport. Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kashe gobarar dake Kano PFS Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga jaridar Nagartacciya a daren juma'ar nan, inda yace bayan faruwar al'amarin ne jam'i'ansu suka kai agajin gaggawa. “Jami'an mu sun isa matatar Mai na NNPC ɗin inda suka iske wata motar dakon Mai ta daki wata motar tankar Mai dukkaninsu ɗauke da Mai inda tsakanin rami da rami ya fashe, inda jam'i'an mu suka bayar da agajin gaggawa ba tare da wuta ta tashi ba, "in ji PFS Saminu Yusif”. Saminu Yusuf ya kuma ce jam'i'an su sun isa Sheka Aci Lafiya da ƙarfe 03:35 na yammacin Juma'a, inda suka tarar da tashin gobara a cikin wani Gida mai hawa ɗaya, inda Ɗakuna kwana guda uku, Falo guda 1, sai Ɗakin Girki guda ɗaya, da Banɗaki dukkaninsu sun ƙone ƙurmus. Jaridar Nagartacciya ta rawaito cewar hukumar kashe gobarar ta jihar Kano ta kuma ce ta samu kashe wutar a Ɗaki guda ɗaya, inda tace yanzu haka tana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Shin Da Gaske Akwai Halittar Aliens A Duniya

Mutane da dama suna yawan tambayar shin ko da gaske akwai “aliens” kuma yaya suke da makamantansu, saboda sun jima suna jin labaru game da su. Don haka mutane da dama sun shiga shakkun shin da gaske akwai waɗannan halittu; a ina suke, kuma yaya suke? Wato “aliens” wasu halittu ne da aka fara tunanin kasantuwarsu a ƙirƙirarrun labarun kimiyya. Ta wannan hanyar ne ma’abota wannan rubutu suka ankarar da masana kimiyya domin a duba yiwuwar kasantuwar waɗannan halittu.  To daman ita kimiyya haka take; wato sai an yi tunanin wani abu kafin a gudanar da bincike a kansa. A cikin tunanin sai aka ce yanzu mutane da suke rayuwa a wannan duniyar ta earth wacce ta kasance ta uku a tsarin hasken rana (solar system), shin mutum ba ya tunanin cewa wataƙila akwai wata duniya da wasu halittu suke rayuwa? Wato yadda abun yake shine samuwar ruwa a wannan duniyar shi ya ba wa duk wata halitta damar rayuwa a cikinta saɓanin yadda sauran duniyoyin da suke a tsarin hasken rana suka kasance. Sannan a lamarin kimiyya kuma shine duk abun da ya faru a wani wuri to ya ta’allaƙa da faruwar wani abu a wani wuri da suke mabanbantan wuri da lokaci. Wannan shi ne abun da masanin kimiyya Einstein yake yi wa laƙabi da “spooky action at a distance”, wanda shi ne dai abun da sauran masana suka ƙira da “quantum entanglement.” Sai wadannan masu hasashen suka ce matuƙar akwai irin waɗannan nazariyyoyin a kimiyya tabbas hakan yana ƙara nuna cewa ba zai yiwu ace mu kaɗai ne muke rayuwa a faɗin ƙaunu ba. Wataƙila akwai wasu a wata ƙaunun (parallel universe) da suke rayuwa –ko da ace ba kamar mu suke ba to za su kasance wasu halittu ne daban. Wannan duk ya fara ne daga tunanin maƙirƙira labarum kimiyya da ake ƙira “science fiction”, musamman waɗanda suka karanci kimiyya. Sai suka samar da kalmar “aliens” tare da wasu kalmomi waɗanda suka danganci juna. Bayan duk waɗannan sai masana kimiyya suka ƙara ƙaimi wajen bincike kan sanin haƙiƙanin kasantuwar waɗannan halittu da aka yi hasashen kasantuwarsu –shin a ina suke? Kuma yaya suke? Waɗannan tambayoyi har yanzu babu wanda zai bayar da amsarsu domin babu wata hujja ƙarara da ta nuna cewa wani masani ya taɓa cin karo da waɗannan halittu a yayin bincike a sararin samaniya. Har tauraron Ɗan-Adam aka ƙirƙira aka harba sararin samaniya domin farauto wata hujja ta bayani dangane da kasantuwar “aliens” a sararin samaniya. Sai dai akwai wasu bayanai da suke nuna cewa “aliens” sun taɓa zuwa wannan duniyar, har ma sun taɓa zuwa kauyen Dulali na ƙaramar hukumar Darazo a jihar Bauchi a jirginsu. Haka wani bincike ma ya ƙara nuna cewa an taɓa ganin wani abu da ake kyautata zaton jirgin waɗannan halittun ne a garin New Jersey na ƙasar US a shekarar 1952. Wasu sun yarda da haka wasu kuwa ba su yarda ba. Idan Allah Ya kai mu zan kawo muku labarin wanda “aliens” suka sace shi kuma suka dawo da shi bayan wasu shekaru. Mohiddeen Ahmad

Yadda Aka Tsinci Wata Jaririya A Kano

Yanzun nan da ranar juma'ar nan muka samu labarin cewar an ajiye wata jaririya a kofar wani gida dake ungwar Nalado cikin tukuntawa a jihar Kano. Sai dai ko da aka tuntubi matan gidan da wasu daga cikin matasan gidan waɗanda ake maƙotaka dasu, sunce basu da masaniya kan mahaifiyar yarinyar, hasalima basu san daga ina aka dakko yarinyar aka ajiye ba. Wata mata mai suna Lantana da aka zanta da ita tace “bayan mun ga jaririyar da aka ajiye a zauren gidan mu mun mata wanka tare da saka mata sutura, "inji matar”. Sai dai mai ungwar na tukuntawa ya hana yan jarida ɗaukar abubuwan da suka faru, ko mainene dalilai? Allah Masani!!! @Abdussamad Ishaq